Ɗaya daga darussa masu muhimmanci a rayuwa shine: "Ya kamata mutum yayi ƙoƙari ya zama karbabbe a gurin Allah, kuma ya yi iya ƙoƙarin sa ba tare da ya damu da ra’ayin mutane game da shi ba".
Daren Nisfu Sha’aban Mai girma da ɗaukaka yana cewa: (Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku da Aljanna wacce fādinta ya kai sammai da ƙasa, wacce aka tanadar wa masu tsoron Allah) Aali Imran: 133. Sheikh Ṣaduq ya rawaito da ingantaccen isnadi daga Hariz as-Sijistani daga Zurara bin A‘yun, ya ce: Na tambayi Abu Ja‘afar (A.S) cewa: Me zaka ce game da daren Nisfu Sha’aban? Sai ya ce: “Allah Maɗaukaki yana gafarta wa halittunsa a wannan daren fiye da adadin gashin awakin ƙabilar Kalbiy, kuma Allah Maɗaukaki yana saukar da mala’ikunSa zuwa saman duniya da kuma ƙasa a Makka.” Kuma an rawaito da isnadi mai inganci daga Hasan bin Faḍḍal, ya ce: Na tambayi Ali bin Musa ar-Riḍa (A.S) game da daren nisfu Sha’aban, sai ya ce: “Dare ne da Allah ke ‘yantar da wuyoyi daga wuta, kuma Yana gafarta manyan zunubai.” Sannan ya ce: “Ku yawaita ambaton Allah Maɗaukaki, da neman gafara da yin addu’a a cikinsa, domin mahaifina (A.S) yana cewa: Addu’a a wannan daren karɓaɓɓiya ce.” Kuma an rawaito daga al-...
Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa). Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...
Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan. A lokacin da Sayyid Muhammad Baƙir Sadr yake neman ilimi Ƙanwarsa Bintul Hudah tace: "Na kasance tare da ɗan'uwana a wancan lokacin muna tattara kuɗin da muke samu, koda kuwa kaɗan ne, sai Sayyid ya sayi littafi da su, mu karanta mu fahimta. Daga baya sai ya sayar da littafin domin ya sayi wani. Haka muka ci gaba da rayuwa bayan hijirarmu zuwa Najaf al-Ashraf" - Amma daga ƙarshe mai ya faru? Ilimin shi Sayyid Muhammad Baƙir Sadr (QS) da rubuce rubucen shi sun gajiyar da masu bincike, saboda duk wani mai ilimi da ya karanta littattafansa sai ya jinjina masa, ga kaɗan daga shaidan manyan Malaman Shi'a a kansa: - Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Abul Qasim Al-Khuʾi (QS) yace: "Lallai Najaful Ashraf tana alfahari da Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Lallai Allah Maɗaukaki Ya bai wa wannan Sayyid abin da bai ba wa wani ɗalibina ba." - Sayyid Ruhullah Al-Musawi Al-Khumaini (QS) yace: "Sayyid Muhammad Baqir Sadr yana daga cikin fitattun M...
Comments
Post a Comment