- Addinin musulunci ya tausayawa Mace yayin da ya sauƙe ciyarwan ƴayan ta da mijin ta da iyayen ta daga kanta, hatta ciyar da kanta bai daura mata ba, ya wajabtawa iyayen ta ne a yayin da take tare dasu, ya ɗaurawa mijin ta a yayin da tayi aure.
- Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sanya wajibcin bata cikakken sadaki, bai wajabta mata bada ko sisi ga miji ba.
- Ya tausayawa mace a yayin da yace wa ɗa, "Mahaifiyar ka! Mahaifiyar ka!! Mahaifiyar ka!!! Sannan mahaifin ka", duka don girmamawa gare ta.
- Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sauƙe mata farillan hajji muddin bata tare da mijin ta ko wani muharrami da zai tsare ta har zuwa dawowan ta.
- Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sanya bata gadon mijin ta, dana ƴan uwan ta, dana ƴayan ta, da na iyayen ta, duk kuwa da cewa babu nauyin ciyarwan kowa a kanta.
- Musulunci ya tausayawa mace tare da girmamawa gareta a yayin da ya haramta ingancin auren ta babu waliyyi da shaidu, duka saboda kada a zarge ta ko a zubar mata da mutunci da bata silsilan ƴayan ta.
- Musulunci ya tausayawa mace tare da girmamawa gareta a yayin da wajabta bulala tamanin (a bainar jama'a) ga wanda yayi mata ƙazafi, sannan shaidar sa ba karɓaɓɓiya bace daga wannan rana.
- Musulunci ya tausayawa mace tare da girmamawa gareta a yayin da ya sanya wanda ya mutu wajen kare mutuncin ta shahidi.
- Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sanya hatta bayan mutuwan ta babu mai mata wanka sai mijin ta ko makusanta gareta.
- Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sanya likafanin ta fiye da na namiji, za'ayi mata sutura da likafani yanki biyar, duka saboda suturce alfarman ta.
Aminci da rahama da albarka su tabbata ga wanda ya karanta ya yaɗa shi domin amfanar wasun mu, da yaye wahamin dake zukatan masu ganin Allah ya kaskanta mace.
3rd November 2022.
© E m r a n D a r u s s a l a m.
Comments
Post a Comment