🌻 إلهي بفاطمة (عليها السلام)
💡 Sheikh Nasrallah shah Ãbaadi yace: mahaifina (Shah Ãbaadi ya kasance yana cewa: (Ku kula da muqamin sayyida Fatima Zahra (AS) mai girma a nafilolin ku na dare, sannan kusani cewa tawassili da ita yana qara kusanci ga Allah, sannan yana qara sa bawa ya zama ya qara sanin ubangiji madaukaki, sannan kada ku manta yi mata salati kafin kiran sallan asubah).
Yaci gaba da cewa:(Haqiqa asasin addini shine son sayyida Fatima (AS) haqiqanin musulunci kuma shine qin maqiya sayyida Fatima (AS), wanda yaso sayyida Fatima (AS) yaqi maqiyanta shine musulmi.
✨ Sannan ya kasance yana son sharifai (wadanda suka fito daga zuriyan sayyida Fatima) ya kasance idan yayi istihara sai yace: "Ya ubangiji dan tsarkin sayyida zahra, don hasken Zahra, don muqamin sayyida zahra kayi min kaza, haka nan idan ya karanta Qur'ani.
✨ Ya Allah ka bamu domin sayyida zahra (AS).
© 07/01/2022
© Emran Darussalam
© imrandarussalam99@gmail.com
Comments
Post a Comment