Skip to main content

Posts

Showing posts from June, 2025
كيف يجب أن تكون سيرة الطالب الحوزوي؟ يقول الفقيه الميرزا جواد التبريزي [طاب ثراه]: 📚 الطالب في سبيل طلب العلم الديني، لا ينال التوفيق الحقيقي إلا إذا قرن الجدّ والمثابرة في دراسته، وحرص على تهذيب نفسه وتزكيتها، وكان في الوقت نفسه محبًّا حقيقيًا لأهل البيت (عليهم السلام). 🚫 فالمحبة اللسانية أو المظاهر الشكلية لا تكفي، بل لا بدّ أن يُجسّد هذه المحبة بسلوكه وعمله وأخلاقه. ❤️‍🔥 وإظهار المحبة والمودّة لأهل البيت (عليهم السلام) يمكن أن يكون بوجوه شتّى، وأهمّها: إحياء شعائرهم، وإلقاء الخطب في مآتمهم، وبيان مظلوميتهم للناس، ونشر فضائلهم ومقاماتهم بكلّ وسيلة ممكنة. 📖 والقرآن الكريم يرشدنا إلى ذلك في قوله تعالى: ﴿وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ﴾ [المائدة: 35] فاطلبوا إلى الله الوسيلة. 🌟 ولا شكّ أنّ أعظم وسيلة إلى الله هم أهل البيت (عليهم السلام)، فالتوفيق بيد الله، وأبواب الفيض الإلهي هم، والوسيلة الأسمى للتقرّب إليه. 🕊 وإذا نظرتَ في سِيَر العلماء الكبار، ترى أن سرّ نجاحهم لم يكن في الجدّ العلمي فحسب، بل في الإخلاص، وشدّة الولاء، والارتباط القلبي، والتوسّل المستمرّ بأهل البيت (عليهم السل...

Labari Mafi Ƙayatarwa A Ranar Gadir.

Hassan ya kasance ɗan shi'a kuma dalibi a makarantar da mafi yawan ɗaliban ta Ahlussunnah ne. Wata rana malami zai fita daga aji sai yace: Ya kai Hassan taso ka zauna a gurin zama na, kada ka yarda da wani rikici ko suruce-suruce a tsakanin ɗalibai har zuwa dawowa na!. Sannan yayi musu umurni akan suyiwa Hassan ɗa'a kuma suyi masa biyayya! A nan ne Hassan ya tashi tsaye sai yacewa Malamin: Shin zai iya yiwuwa inyi tambaya? Malami yacewa Hassan Bismillah, zaka iya tambayar ka! Sai Hassan yace: Kunce Annabi (S) yabar duniya ba tare da ya ayyana kalifa a bayansa ba, shin Annabi (S) bai kai malaman mu (Masu girma) ilimi da tsantseni da sanin ya kamata bane? Tunda kunce bai ayyana wanda zaici gaba da tafiyantar da al'amuran addini a bayan sa ba, kuma bai sanya wanda zai ci gaba da hana rikici tsakanin al'ummar musulmi da daular ubangiji a bayansa ba?!!  Dukda cewa malam kasan zaka dawo anjima amma ka daura ni a matsayin kalifa a bayan ka, to taya Annabi (S) da ya...

Tasirin Ƙarfin Allah Akan Kowa Da Komai

Shah na Iran ya kore shi, jam’iyyar Ba’ath ta Iraki itama haka, gwamnatin Kuwait ta hana shi shiga kasarta. Marji'in addini ne, abin so ga al’umma, Yana cikin hamada shi kadai tare da Sayyid Ahmad ɗansa. Dukda haka bai karaya ba, ya dogara da Allah. An ɗauki wannan hoton na alwalarsa, domin tarihi ya sani cewa: idan gwamnatoci sun tasar maka, hanyoyi suka rufe, kuma miyagun ƙarfi suka haɗu domin gamawa da kai — idan Allah yana tare da kai, zaka kasance cikin natsuwa ba tare da tsoro ba, kuma zaka yi nasara da addu’ar Imam Mahdi (Atfs ). Allah ya yi maka rahama ya Imamu (QS).

Muhimmancin Ranar Arfa A Imamiyya.

Da Alƙalamin Sheikh Imrana Darussalam  Azumin Arfa (ranar 9 ga Zul-Hijja) yana da matsayi mai girma a tsarin ibada na Imamiyya (Shi'a), kodayake yana da bambanci kadan da fahimtar Ahlus-Sunna. A mad'hab din Imamiyya, wannan rana tana da daraja ta musamman saboda kasancewarta rana mai tsarki, rana ta addu'a da tuba, kuma rana ce da Allah ke gafartawa bayinsa da dama, musamman ga wadanda ke Arafat da kuma wadanda ba su je Hajji ba. 1. Muhimmancin ranar Arfa a Imamiyya Ranar Arfa ita ce rana ta biyu mafi falala a cikin shekara bayan Laylatul Qadr. Shi’a Imamiyya suna ganin cewa wannan rana ita ce ranar kusanci da Allah, inda ana karanta addu'o'i da yawa, musamman Addu'ar Imamu Husain (a.s) a ranar Arfa da kuma Addu’ar Imam Zainul Abidin (a.s), wadanda suka kunshi falsafa mai zurfi da ruhaniya mai karfi. 2. Azumi a ranar Arfa a Imamiyya Azumin ranar Arfa yana da falala mai girma ga wanda ba ya aikin Hajji, kamar yadda ya zo a hadisan Ahlul Bayt (a.s). Ha...

Darasi

"Wanda ke kula da tururuwa a cikin duhu rami... Kana tsammani ko tunanin wata rana ya manta da kai... Ka ji da yaƙini cewa a ko da yaushe yana sane da kai, kuma yana jiran ka kira shi ya amsa maka, ka roƙe shi ya biya maka buƙatu. Mafificin lokacin amsa kiran bayi da biya musu buƙatu shine dare, a sanda idanu suka yi bacci, shi ko a lokacin ya ke shela cewa: "Wa ke da buƙatu a cikin bayina"!!! Ya Allah ka yi mana abinda ya ke shine alkairi a gurinka, ka tabbatar da mu cikin yi maka ɗa'a. 04/05/2024, Emran Darussalam

WULAƘANTA MUMINI

Manzon Allah (S) ya ce: "Wanda ya wulakanta wani muminin namiji ko mace, ko ya raina shi saboda talaucinsa ko rashin abin hannunsa, Allah Madaukaki zai tona asirinsa a ranar Alƙiyama sannan ya kunyata shi." ¹ A wani faɗin (mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce: "Ku sani, wanda ya raina wani miskini Musulmi, to haƙiƙa ya yi sako-sako da hakkin Allah ne, kuma Allah zai yi sako-sako da shi a ranar Alƙiyama, sai dai idan ya tuba." Kuma ya ce (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa): "Wanda ya girmama miskini Musulmi, zai haɗu da Allah a ranar Alƙiyama alhali yana mai yarda da shi." ² Ha'ilau an ruwaito daga Imam Ja'afar Sadiq (AS) yace: "Wanda ya haɗu da faƙiri musulmi (talaka ), ya yi masa sallama saɓanin yadda yake yi wa mai arziki sallama, zai haɗu da Allah Madaukaki a ranar Alƙiyama alhali Allah yana mai fushi da shi" ³ 1 - Bihar Al-anwar, Juz'i na 44 Shafi na 52. 2 - Bihar A...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...