Daga Kyawawan Dabi'un Imam Aliyu Zainul Abidin (AS) Imam Zainul Abidin (A.S.) ya kasance yana sa ido da kula kan ayarin mahajjata da ke zuwa daga wurare masu nisa suna ratsa birnin Madina. Wata rana ya shiga cikin ɗaya daga cikin ayarin da suka taho, yana mai ce musu yana so ya yi aiki a matsayin bawa mai yi wa mahajjata hidima. A wancan lokaci ana yin tafiya ne a kan dawakai da rakuma, kuma tafiyar tana ɗaukar kwanaki goma ko fiye. A duk wannan lokaci, Imam (A.S.) yana mai da hankali sosai wajen yi wa mahajjata da matafiya hidima, da biya musu bukatu da bin umarninsu. Wata rana a hanya sai ayarin da Imam yake tare da su suka haɗu da wani da ya san shi. Mutumin ya yi matuƙar mamaki da abin da ya gani, Imami yana hidima wa ayarin mahajjata, sai ya tambayi mutanen ayarin cewa: “Wane ne wannan da kuka taho tare da shi yana yi muku hidima a hanya?” Sai suka ce: “Hakika ba mu san shi ba; wani kyakkyawan saurayi ne muka haɗu da shi a Madina, ya ba mu kansa don ya yi mana hidima, sai muk...