A cikin Tafsirin Al-Mīzān na Allāma Ṭabāṭabā’ī, abin da ake nufi da faɗin Allah Madaukaki:
إِذْ جَاءَ رَبَّهُ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ
shi ne:
“zuciyar da babu wata alaƙa a cikinta da wani abu face Allah kaɗai.”
Ƙarin bayani kan maganar Allāma kuwa shi ne:
"ba ma’anarta shine wannan zuciya ba ta son wani sai Allah kaɗai ba, domin babu laifi son wanin Allah. Amma abin da ake nufi shi ne zuciyar ta kasance tana da mafi ƙarfin alaƙa da ƙauna ga Allah fiye da komai da kowa, kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce:
وَالَّذِينَ آمَنُوا أَشَدُّ حُبًّا لِلَّهِ
“Waɗanda suka yi imani su ne mafi tsananin soyayya ga Allah.”
21/01/2025,
Comments
Post a Comment