Skip to main content

Kwaɗaitarwa Kan Azumin Ranar Arfa da Ayyukan Cikinta

Kwaɗaitarwa Kan Azumin Ranar Arfa da Ayyukan Cikinta

Ranar Arfa tana daga cikin mafi girman ranaku a Musulunci, rana ce ta rahama, gafara, karɓar addu’a da kusanci ga Allah Maɗaukaki. Ita ce ranar tara ga watan Zul-Hijja, ranar da mahajjata suke tsayuwa a filin Arfa suna roƙon Ubangijinsu cikin tawali’u da kuka.

An rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekara biyu; shekarar da ta gabata da kuma mai zuwa. Wannan wata babbar dama ce ga masu neman gafarar Allah da tsarkake zukata.

Falalar Azumin Ranar Arfa
Azumin ranar Arfa na daga cikin ibadun da malamai suka yi matuƙar kwaɗaitarwa a kansa ga waɗanda ba sa aikin Hajji. Rana ce da:
Allah ke yawaita ‘yanta bayinsa daga wuta.
Addu’o’i suke samun karɓuwa.
Rahama da albarka suke sauka.
Zuciya take samun nutsuwa da kusanci ga Allah.

Saboda haka kada mu bari wannan rana ta wuce ba tare da:
azumi,
addu’a,
istigfari,
salati ga Annabi da Ahlulbaitinsa (A.S),
karatun Alƙur’ani,
da yawaita ambaton Allah ba.

Muhimman Ayyukan Ranar Arfa
1. Azumi
Ga wanda ba ya aikin Hajji, yana da matuƙar falala ya azumci ranar.
2. Addu’a
Ranar Arfa rana ce ta addu’a. Daga cikin shahararrun addu’o’in ranar akwai:
Addu’ar Imam Husain (A.S) ta Arfa.
Yawaita “Astaghfirullah”.
Roƙon Allah biyan buƙatu da gafarar zunubai.
3. Karatun Alƙur’ani
A ware lokaci domin karanta Alƙur’ani tare da tunani da natsuwa.
4. Sadaka da taimakon mabukata
Yin alheri a wannan rana yana da lada mai yawa.
5. Tuba ta gaskiya
Mu yi anfani da wannan rana wajen komawa ga Allah da barin zunubai da sabunta niyyar rayuwa ta gari.
Saƙon Tunatarwa
Wataƙila wannan ce Arfarka ta ƙarshe, kada ka bari ta wuce cikin shagaltuwa da abubuwan duniya. Ka ɗaga hannuwanka zuwa sama, ka roƙi Allah cikin zuciya mai tawali’u, domin akwai mutane da dama da shekarar da ta gabata suna tare da mu, amma yau babu su.

Allah Ya sa mu dace da azumin ranar Arfa, Ya karɓi addu’o’inmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya sanya mu cikin bayinsa na gari.

اللهم اجعلنا من عتقائك من النار في يوم عرفة.

Mon, May 25
2026.
Emran Darussalam.

Comments

Popular posts from this blog

Daren Nisfu Sha’aban

Daren Nisfu Sha’aban Mai girma da ɗaukaka yana cewa: (Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku da Aljanna wacce fādinta ya kai sammai da ƙasa, wacce aka tanadar wa masu tsoron Allah) Aali Imran: 133. Sheikh Ṣaduq ya rawaito da ingantaccen isnadi daga Hariz as-Sijistani daga Zurara bin A‘yun, ya ce: Na tambayi Abu Ja‘afar (A.S) cewa: Me zaka ce game da daren Nisfu Sha’aban? Sai ya ce: “Allah Maɗaukaki yana gafarta wa halittunsa a wannan daren fiye da adadin gashin awakin ƙabilar Kalbiy, kuma Allah Maɗaukaki yana saukar da mala’ikunSa zuwa saman duniya da kuma ƙasa a Makka.” Kuma an rawaito da isnadi mai inganci daga Hasan bin Faḍḍal, ya ce: Na tambayi Ali bin Musa ar-Riḍa (A.S) game da daren nisfu Sha’aban, sai ya ce: “Dare ne da Allah ke ‘yantar da wuyoyi daga wuta, kuma Yana gafarta manyan zunubai.” Sannan ya ce: “Ku yawaita ambaton Allah Maɗaukaki, da neman gafara da yin addu’a a cikinsa, domin mahaifina (A.S) yana cewa: Addu’a a wannan daren karɓaɓɓiya ce.” Kuma an rawaito daga al-...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan.

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan. A lokacin da Sayyid Muhammad Baƙir Sadr yake neman ilimi Ƙanwarsa Bintul Hudah tace: "Na kasance tare da ɗan'uwana a wancan lokacin muna tattara kuɗin da muke samu, koda kuwa kaɗan ne, sai Sayyid ya sayi littafi da su, mu karanta mu fahimta. Daga baya sai ya sayar da littafin domin ya sayi wani. Haka muka ci gaba da rayuwa bayan hijirarmu zuwa Najaf al-Ashraf" - Amma daga ƙarshe mai ya faru? Ilimin shi Sayyid Muhammad Baƙir Sadr (QS) da rubuce rubucen shi sun gajiyar da masu bincike, saboda duk wani mai ilimi da ya karanta littattafansa sai ya jinjina masa, ga kaɗan daga shaidan manyan Malaman Shi'a a kansa: - Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Abul Qasim Al-Khuʾi (QS) yace: "Lallai Najaful Ashraf tana alfahari da Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Lallai Allah Maɗaukaki Ya bai wa wannan Sayyid abin da bai ba wa wani ɗalibina ba." - Sayyid Ruhullah Al-Musawi Al-Khumaini (QS) yace: "Sayyid Muhammad Baqir Sadr yana daga cikin fitattun M...