Ta Yaya Albarka Ke Ƙaruwa A Gida?
Amirul Muminin Ali (a.s) ya ce: (Gidan da ake karanta Alqur'ani a cikinsa, kuma ake ambaton Allah Ta'ala, albarkarSa tana yawaita, Mala'iku suna halartarsa (cikin gidan), shaidanu suna barinsa, kuma (gidan) yana haskakawa ga mazauna sammai kamar yadda taurari ke haskakawa ga mutanen ƙasa, amma gidan da ba a karanta Alkur'ani a cikinsa, kuma ba a ambaton Allah, albarkarsa tana raguwa, kuma mala'iku suna barinsa, shaiɗani suna halartan gidan.
Masdar: Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 499.
27/05/2024,
Comments
Post a Comment