Ina Ɗaliban Ilimi???
Sheikh Muhammad Taƙi Bahjah (QS) yace: Ta hanyar ƙwarewa, ya zama abu sananne gare ni cewa: "idan ba'a sami sakaci a cikin lamuran ibada ba, to za a iya kammala darasin da ke bukatar yin awa ɗaya cikin mintuna goma! (tare da fahimta)"
Allah yana cewa: "Kuma kuji tsoron Allah da takawa, sai Allah Ya sanar da ku" – Baqarah, aya 282.
Sharhi:
Wato a yayin da bawa ya kula da janibin ibada tare da tsoron Allah, zai sami saurin fahimta a janibin karatu, zai fahimci karatu cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da shan wahala ba.
05/06/2024,
Comments
Post a Comment