🌹✨ RANAR JADDADA MUBAYA'A DA ABOTA – RANAR GHADIR ✨🌹
💚 Ɗan uwa zo Mu Sake Jaddada Abota da Ƴan'uwantaka Kan Wilayar Amirul Muminina Imam Ali (A.S.) 💚
🤝📜 Ni Emran Darussalam Ina cewa gare ka:
"Na ƙaunace ka saboda Allah, na yi abota da kai saboda Allah, kuma na yi alkawari da Allah, Mala'ikunsa, Littattafansa, Manzanninsa da Imamai Ma'asumai (A.S.) cewa idan na kasance daga cikin mutanen Aljanna kuma aka ba ni izinin shiga Aljanna, ba zan shiga ba sai tare da kai."
💐 Ɗan uwa ka amsa da:
✨ "Na karɓa." ✨
🤲 Sannan:
"Na yafe maka dukkan haƙƙoƙin 'yan'uwantaka da ke tsakanina da kai, sai dai tabbatuwa a kan Wilayar Amirul Muminina Imam Ali (A.S.) da sauran Ahlulbaitin Tsira (A.S.), da kuma haƙƙin shafa'a, addu'a da ziyara."
💚❓ _Shin ka karɓa?_ ❓💚
🌺 Wannan wata kyakkyawar al'ada ce ta ranar Eidul Ghadir, wadda ke ƙarfafa zumunci, soyayya da haɗin kai saboda Allah. A wannan rana, mabiya Ahlulbaiti (A.S.) suna sabunta mubaya'a ga Wilayar Imam Ali (A.S.), suna kuma yi wa juna alkawarin aminci, addu'a, taimakon juna da tuna juna har zuwa Lahira.
🌹 Eidul Ghadir Mubarak! 🌹
💚 Allah Ya tabbatar da mu a kan Wilayar Muhammad da Alayen Muhammad (S.A.W.A.), Ya haɗa zukatanmu cikin ƙauna da ƴan'uwantaka saboda Shi. 🤲✨
Thu, Jun 4
2026.
Comments
Post a Comment