Yazo a Ruwaya daga Ahlul-Baiti (a.s): 🔹 Imam Ja’far as-Sadiq (a.s) ya ce: “Mamaci yana farin ciki da addu’a da sadaka kamar yadda mai rai yake farin ciki da kyauta.” 📚 _Al-Kāfi, Shaykh al-Kulaynī, juzu’i 3, shafi 230._ Imam Ali (a.s) ya ce: “Kada ku yanke addu’a ga matattanku, domin suna jiran addu’arku.” 📚 _Nahj al-Balagha, hikima 130 (ma’ana)._ Ya Allah Ka Jiƙan Iyayenmu Da Rahma.
Faƙihin Malamin nan Ayatullahi Shaykh Lutfullah as-Safi al-Gulbaygani (QS) ya ce: Al-Intizār (Jira) makaranta ce kuma babbar jami’a ta tsarkake zuciya da gina kai da ruhi. Dole ne ga wanda ya danganta kansa da wannan manhaji ya zamto tsayayye tsayuwa da ƙarfi, kuma ya zamto mai aikata abin da ke cikin Du'a al-Ahd a inda muke cewa: mu “masu gaggawar zuwa gare shi ne wajen biyan bukatunsa …”; wato (mai jiran zuwan Imam Mahdi) wajibi ne ya yi ƙoƙari sosai wajen biyan bukatun Waliyul Asr, Allah Ya gaggauta bayyanarSa. Masu jiran Imam al-Hujja (Atfs) su kiyaye addininsu, su tsare iyalansu da matasansu daga karkacewa da ɓata, kuma su himmatu wajen biyan bukatun muminai; domin a gaskiya waɗannan su ne bukatun Imamin Zamansu (Atfs). Ayyuka A Lokacin Intizar: - Tsayuwa kan Sallar farilla Yin salla a kan lokaci, musamman sallar jam’i idan akwai dama. Domin salla ita ce ginshiƙin addini kuma tana tsare mutum daga karkacewa. - Addu’a musamman domin gaggauta bayyanarsa: Du'a al-Faraj: “Alla...