Wahabiyanci da wanda ya assasashi: - Ana nasabta firƙan wahabiyya ne ga Muhammad bin Abdulwahab Bn Sulaiman Annajdi, wanda aka haifa a shekarar 1115 Hijiriyya, ya rasu a shekarar 1206 Hijiriyya. Yayi karatun addini daidai gwargwado, kamar yadda a bayyane yake ya kasance mai yawan bibiya da muɗala'an labaran da suka shafi Musailama al-kazzab, da Sajah, da Aswadul Anasi, da Ɗulaiha Al-asadi, wanda tsatstsauran ra'ayin shi ya fara bayyana tun lokacin da yake karatu, mahaifin sa da wasu daga malaman sa su suka fara yaƙar wannan ra'ayi nashi, suka nuna a nisance shi, inda suke cewa: "Wannan zai ɓata, kuma zai ɓatar da dukkan waɗanda suka nisanci Allah kuma suka kasance shaƙiyyai". A shekarar 1143 Hijiriyya ya bayyana da'awar sa zuwa ga sabuwar mazhabin sa, amma mahaifin sa da wasu daga malaman sa suka yi ƙoƙarin tsaida shi tare da tunkarar sa, suka karya karsashin kiran nasa, har zuwa lokacin da mahaifinsa ya rasu a shekarar 1153 Hijiriyya, a nanne ya s...