- Addinin musulunci ya tausayawa Mace yayin da ya sauƙe ciyarwan ƴayan ta da mijin ta da iyayen ta daga kanta, hatta ciyar da kanta bai daura mata ba, ya wajabtawa iyayen ta ne a yayin da take tare dasu, ya ɗaurawa mijin ta a yayin da tayi aure. - Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sanya wajibcin bata cikakken sadaki, bai wajabta mata bada ko sisi ga miji ba. - Ya tausayawa mace a yayin da yace wa ɗa, "Mahaifiyar ka! Mahaifiyar ka!! Mahaifiyar ka!!! Sannan mahaifin ka", duka don girmamawa gare ta. - Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sauƙe mata farillan hajji muddin bata tare da mijin ta ko wani muharrami da zai tsare ta har zuwa dawowan ta. - Musulunci ya tausayawa mace a yayin da ya sanya bata gadon mijin ta, dana ƴan uwan ta, dana ƴayan ta, da na iyayen ta, duk kuwa da cewa babu nauyin ciyarwan kowa a kanta. - Musulunci ya tausayawa mace tare da girmamawa gareta a yayin da ya haramta ingancin auren ta babu waliyyi da shaidu, duka saboda kada a za...