Skip to main content

Posts

Showing posts from June, 2023

Bayyanar Imam Mahadi

An ruwaito daga manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Lallai bala’i zai sami wannan al’umma, har sai mutum ya rasa mavoya daga zalunci, sai Allah ya tashi wani mutum daga zuriyata daga ‘ya’yan gidana, ya cika qasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. Masdar:  Muntahabul asar: 422, fasali na shida, babi na biyu. Da kuma:  Biharul Anwar, j 52: 336. Ya Allah ka gaggauta bayyanar Imam Mahadi (Atfs).

DAGA TASKAR MAGABATA NA 10.

A Sa'oin Ƙarshe Na Rayuwar Ka Me Kake Ga Shi Zaka Aikata Domin Ya zamto Aikin Ka Na Ƙarshe A Wannan Duniya. Sheikh Ãdil Ãli Jauhar yace: "Wani daga ɗaliban Sayyid Mahdi Shirazi (R) ya naƙalto cewa: Watarana kafin fara darasi na samu Sayyid nace masa: "Ina da tambaya da nake bukatar amsar ta, ina fatan zaku bani lokacin ku, sannan ina neman uzuri idan amsar wannan tambaya tawa ta zamto ba muhimmiya ba a gurin ku. Sai Sayyid yace: Tafaddal, yi tambayar ka. Sai nace: Misali Sayyid kasan cewa zaka bar duniya nan da awa guda ko kwana ɗaya, me zaka aikata a iya waɗannan lokuta da suka rage maka a rayuwa, sannan wane aiki ne zaka yi saurin aikata shi? Sai sayyid ya amsa min cikin sauri ba tare da jinkiri ba (a al'adar Sayyid ya kasance idan akayi masa tambaya sai ya ɗan ɗau lokaci kafin ya bada amsa), amma a wannan lokaci babu jinkiri sai ya amsa da cewa: "Bazan aikata wani aiki ba sai wannan da nake yi yanzu" (ya kasance a lokacin yana muɗali'an litattafin jaw...

Malamai Magabata.

Malamai magabata waɗanda suka rayu a zamanin da ya gabata, sun kasance dukkanin su sunyi nasarar samun ilimi da aiki dashi, sunyi rayuwa mai albarka, kuma suka kuɓuta daga karkata na rayuwa da fikira, duka wannan ya samune bisa sababin cin halal da nisantar abincin haram da ya kasance akwai shubuha a cikin sa. ~ Sheikh Bahjah (QS). Emran Darussalam

JAGORA ABIN KOYI SHEIKH MUHAMMAD NUR DASS (H).

Hujjatul Islam Sheikh Nur Dass (H) Malami ne na shi'a, kuma wakilin Babban Marji'i Ayatullah Sayyid Ali Khamnei (DZ) bangaren Shari'a a Najeriya, wakilcin da ba'a taɓa samun irin sa ba a kaf Nahiyar Afrika. Yana daga cikin ƙoƙarin shi a Najeriya: Assasa Mu'assasar RASULUL A'AZAM FOUNDATION (RAAF), wacce ta kasance mu'assasa ce ta Shi'a Zallah tare da yima wannan Mu'assasar rijista a hukuman ce, ta cika sharruɗa dukkan sharruɗa. Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Mu'assasa ce dake buɗe makarantun Hauzozin ilimi da markazozi dan yada addinin musulunci cikin shi'anci tsantsa, tana da Makarantun Hauzozi da Masallatai a jihohi daban daban a faɗin Nigeria, kuma duka makarantu ne masu rijista waɗanda aka gina akan tsari, kuma makarantu ne da aka yi musu ginin zamani. Tana da keɓantaccen sashe na abinda ya shafi kira da tabligh, wannan sashe ya tara muballigai (Masu isar da sakon musulunci) da yawa a karkashin sa, duka dan Isar da sakon...

DAGA TASKAR MAGABATA NA 9

Natijar cikar kamalar mutum. Daya daga ɗaliban Sheikh Bahjah yace masa: "Yayi mafarki da daya daga ɗaliban Sheikh din yana Sallah a waje mai daukaka, amma a yayin da ya kasance yana sujjada duwatsun wajen sun kasance suna tasbihi tare da shi!! Sai Sheikh Bahjah ya amsa masa da cewa: "Idan mutum ya cika ya kaiga kamala (Samun yardan Allah) zaiji yaga haka a zahiri ba a mafarki ba" 22 October 2022 © Emran Darussalam.

DAGA TASKAR MAGABATA NA 8.

Sheikh Kameel Sulaiman yace: Wata rana Sayyid Hussein Sharfudden ya gayyaci Ruseey cin abinci, a yayin Rusey yazo (Tare da shi akwai iyalan shi) sai ya tarar da babu giya a cikin abincin, sai yaƙi ci duka! Sai sayyid yace masa: Giya haramun ne, sai Rusey yace masa taya giya zai zama haramun bayan da inabi akayi shi, kuma inabi halal ne?! Sai Sayyid ya juya ya nuna ɗiyar sa, yace: Wannan haramun ce a gare ka, bayan mahaifiyar ta takasance halal a gareka - To haka giya ma haramun ne, dukda cewa mahaifiyar ta (Wato inabi halal ne). Nan ya kawo karshen takaddamar. 12 October 20²². © Emran Darussalam. https://Emrandarussalam.websites.co.in

DAGA TASKAR MAGABATA (7)

Sayyid Ku'i (R) a wani muhadaran da ya gabatar a Hauza yake cewa: "Misali: akwai wani birni da cikin sa akwai wasu mutane dake rayuwa cikin duhu mai tsanani, matsaloli kuma suna faruwa dalilin wannan duhun da suke ciki, sarkin garin kuma ya kasance mutum ne mai hikima, sai a binciken sa ya gano fitila da zata iya haskaka garin dukkan shi, sai wannan sarki ya sanya wannan fitila domin mutane su amfana gaba daya, Haka mutane suka yi farin ciki da hakan, bayan wani ɗan lokaci sai aka samu wasu daga mutanen garin suka fasa fitilar, amma da yake shi wannan sarki yana son mutanen sa sai ya sanya wata fitilar daban, sai suka ƙara fasawa, haka ya rinka sanyawa suna fasawa har suka fasa fitilu goma sha daya, sai ya zamto fitila ɗaya tilo ta rage masa, ko yaya zayyi? Idan ya fitar da fitila ta goma shs biyun zasu ƙara fasawa. Hikima da hankali abinda suke cewa anan shine: Kula da wannan fitila shine yafi. Sai wannan sarki ya boye fitilar, yaƙi fitar dashi. Yayi hakane domin ...

DAGA TASKAR MAGABATA (6)

Babban Malamin nan na shi'a wato Sayyid Abdul-A'alah sabzawaari (R) ya kasance yana cewa: "Idan aka goge isnadi da sunan Imamin da aka ruwaito hadisi daga gare shi, kuma aka karanta min yadda matanin hadisin yake, zan iya cewa: Wannan matanin hadisin ya fito ne daga Imami ma'asumi waane (Allah ya qara masa yarda)... Yazo cewa: wataran wani malami ya samo shi, sai ya kawo wani hadisi ya nasabta hadisin zuwa ga Imam Muhammad Baqeer (AS) Sai Sayyid Abdul-A'alah yace masa: Wannan hadisi daka kawo banji kamshin Imam Muhammad Baqeer (AS) a cikin sa ba, kamshin da naji na Imam Ja'afar Sadiq (AS) ne, take aka dauko littafi domin a duba, da aka duba sai aka samu hadisin daga Imam Ja'afar Sadiq (AS) kamar yadda ya gaya musu. Shi yasa ake yawan magana akan shi cewa: A zamanin shi ba'a sami wanda yayi kusa dashi wajen haddace ruwayoyi da isnadi ba, yana da cikakkiyar sani akan abinda ya shafi ilimin hadisi, ta yanda idan ka karanta masa hadisi ba tare d...

DAGA TASKAR MAGABATA (5)

~ Abinda yafi min shine barin wannan duniya!!! Mutuwa tana zuwa wa mutane karo daya (ba tare da sanin su, ko sun shirya ba) suna cikin gafala, zukatan su ya shagala da wasu abubuwan wadanda ba zikirin Allah ba, haka sun manta da mutuwa, a yayin da waliyyai Allah yakan iya sanar dasu ƙarshen su, da lokacin mutuwar su, shi yasa suke zama kullum a cikin shirin tafiya, kamar hikayar da Sayyid Abdulkareem Kashmiri ya hakaito mana cewa: Shekh Ãrif Muhammad Baqeer Qaamusi Albaghdadi yana daga manya Manyan malamai, kuma ya kasance mai tsananin zuhudu (gudun duniya) kuma Ãrifi, ya kasance kamar Sayyid Ali Al-Qadi, wanda ya zamto abin misali a wajen sauran malamai masu tsoron Allah, ya kasance daya daga daliban Mulla Hussein Hamdani Sheikh Muhammad Taha, haka Ayatullah Musnin Hakeem ya kasance daga daliban sa. Ya kasance watarana yana zaune sai akaji yace: "Abinda yafi min shine barin wannan duniyar" Nan aka ga ya fara karanta Suratu yasin, a lokacin da ya iso inda Allah ke...

DAGA TASKAR MAGABATA (4)

Yana warkar da marasa lafiya da isharar hannun sa. Sayyid Abdullah Faɗimi yace: "A shekarun baya akwai wani sayyid a birnin Qom yana warkar da mara lafiya da isharar hannun sa!!! Sai aka tambayi Ayatullah Al-Uzma Sayyid Baha'udden sirrin dake ciki, sai yayi ishara da nannun sa zuwa 'yan laɓɓan sa yace: Hakika shi sayyid ya kasance ya kulle kofofin wuta ne. Abin nufi ya rufe bakin shi daga yin giba da annamimanci da karya da dukkan sabon Allah (Da suka shafi baki) sai Allah ya bashi karaman warkar da mara lfy ta hanyar yin ishara. ___  Dama Allah yace: " Idan ka sallamawa al'amari na zan zamto nine jinka, ganin ka... Allah ka bamu albarkacin masu albarka. ® Emran Darussalam

DAGA TASKAR MAGABATA (3)

Shaheed Mutahhari (R) ya naqalto daga Malamin sa masanin Allah wato Mirza Ali Shirazi yake cewa: "A cikin mafarki na naga cewa gani nan na mutu, a lokacin ne naga ruhi na yabar jiki na, nan fa naga an dauke ni zuwa makabarta, bayan an kaini aka binne ni, haka suka barni ni kadai cikin kabari ina tsoro, kwatsam sai naga kare yana kokarin shigowa cikin kabari na, sai nayi tunanin wannan wani mummunan aiki ne na aikata shi ya fito min a suffar kare, haka nan na shiga damuwa, a wannan lokacin ne Sayyidush-shuhada Imam Hussein (AS) yazo min yace: Kada ka damu domin zan nisantar dashi daga gareka" Daga littafin:  قصص من عالم الأرواح. Shafi na 51. Haka ke nuna Imam Hussein (AS) baya barin wanda yayi ruqo dashi anan duniya. #السلام_عليك_يا_أبا_عبدالله. © 17/2/2022 © Emran Darussalam

DAGA TASKAR MAGABATA 2

🌻 إلهي بفاطمة (عليها السلام) 💡 Sheikh Nasrallah shah Ãbaadi yace: mahaifina (Shah Ãbaadi ya kasance yana cewa: (Ku kula da muqamin sayyida Fatima Zahra (AS) mai girma a nafilolin ku na dare, sannan kusani cewa tawassili da ita yana qara kusanci ga Allah, sannan yana qara sa bawa ya zama ya qara sanin ubangiji madaukaki, sannan kada ku manta yi mata salati kafin kiran sallan asubah). Yaci gaba da cewa:(Haqiqa asasin addini shine son sayyida Fatima (AS) haqiqanin musulunci kuma shine qin maqiya sayyida Fatima (AS), wanda yaso sayyida Fatima (AS) yaqi maqiyanta shine musulmi. ✨ Sannan ya kasance yana son sharifai (wadanda suka fito daga zuriyan sayyida Fatima) ya kasance idan yayi istihara sai yace: "Ya ubangiji dan tsarkin sayyida zahra, don hasken Zahra, don muqamin sayyida zahra kayi min kaza, haka nan idan ya karanta Qur'ani. ✨ Ya Allah ka bamu domin sayyida zahra (AS). © 07/01/2022 © Emran Darussalam © imrandarussalam99@gmail.com

DAGA TASKAR MAGABATA (1)

Sayyid Ali Bahbahani ya nakalto daga daga dalibin Sheikh Murtada Ansari (R) cewa: "Na tafi Najaf domin kammala karatuna na addini, saina samu halartan darasin da Sheikh Murtada Ansari yake gabatarwa, saidai a wannan lokaci naji bana fahimtar darasin yadda yakamata, naji bakin ciki matuka da wannan hali dana tsinci kaina (Na rashin fahimtar karatu) daga karshe dai haka nayi tawassuli da Amirul-muminin Imam Ali Amincin Allah su kara tabbata a gareshi, a daren wannan rana ne nayi mafarki da Imam Ali (AS) har ya karanta min " Bismillahir rahmanir rahim," a kunne na, wayewan gari keda wuya na halarci wajen darasi karo na biyu sai naji ina fahimtar darasin yadda ya kamata, ta kaiga nakanyi tambaya tare da bijiro da mas'aloli wa Sheikh, watarana muna sauraron darasin Sheikh sai ya zamto nayi magana dayawa a yayin darasin, sannan na bijiro da mas'aloli ina fada Sheikh Murtada yana karewa, bayan mun kammala darasi sai Sheikh din ya matso kusa dani, ya kawo bak...

Dukkanin mu akan hanya muke.

Ku sanya farin ciki a zukatan ƴan uwan ku muminai.#Barka_Da_Safiya

Wanda Yake So Yaga Imamul-Hujjah (Atfs).

Zikiri

Sheikh Bahjah (QS) yace: "Suna zuwa gurina suna buƙatar in basu azkār, Shin ƙur'ani bai kasance mafificin zikiri ba".

10 GA WATAN RAMADAN; RANAR JUYAYIN TUNAWA DA WAFATIN UMMUL-MUMININ SAYYIDAH KHADIJAH(AS), MATAR ANNABI MUHAMMAD(SAW):

Ummul-Muminin Khadijah bint Khuwailid(as), matar Annabi Muhammad(saw) tayi wafati ne a ranar 10 ga watan Ramadan shekara ta 10 da aiko Annabi(saw), shekara 3 kafin hijira. Kafin rasuwarta; Khadijah(as) ta ba da gudummawa mai girman gaske wajen kare Annabi(saw) da kuma ci gabantar da Musulunci a lokacin da yake cikin mawuyacin hali. Saboda irin wannan gagarumar gudummawa da Nana Khadijan(as) ta bayar ne; aka ruwaito Manzon Allah(saw) yana cewa: ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻷﻛﺮﻡ(ﺹ): ﻣﺎ ﻗﺎﻡ ﻭﻻ ﺍﺳﺘﻘﺎﻡ ﺩﻳﻨﻲ ﺇﻻ ﺑﺸﻴﺌﻴﻦ: ﻣﺎﻝ ﺧﺪﻳﺠﺔ(ع) ﻭﺳﻴﻒ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ‏(ﻉ) . (ﺷﺠﺮﺓ ﻃﻮﺑﻰ ﺝ 2 ﺹ 20). "Ba don dukiyar Khadijah(as) da takobin Ali(as) ba, da wannan addini bai tsaya da kafarsa ba". (ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﻣﻦ ﺳﻴﺮﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲّ ﺍﻷﻋﻈﻢ 2/121). Wannan shine ma'anar fadin Allah(t) ga Annabi(saw): ﻭَﻭَﺟَﺪَﻙَ ﻋَﺎﺋِﻠًﺎ ﻓَﺄَﻏْﻨَﻰ "Mun sameka marar shi, sai muka wadatar da kai". (Q:93:8). Hakan yana nufin, Annabi(saw) ya samu wadata da dukiya mai yawan gaske da yayi amfani da ita wajen yada Musulunci, sabida tarayyarsa Khadija...